<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>490</hymn_number>
<title>Muna Raira Waƙoƙin Yabo LW490</title>
<lyrics>[V1]
 1) ga Ubangijinmu.
 Muna shaida bishararsa.
 Shi ya sha wahala ya mutu a kan giciye.
 Don duniya ta sami ceto.

[V2]
 KORUS
 Halleluya, Yesu na zuwa don ya karɓe mu.
 In muna da bangaskiya.
 Halleluya ba shakka za mu shiga gidan sama.
 In mun yi zaman, zaman ƙauna.

[V3]
 2) Dukan mu mawaƙa da ka raira waƙoƙi yau.
 Shari'armu mai yawa ce.
 Don muna karantawa muna raira maganarsa.
 Amma ba mu aikatawa fa.
 Korus

[V4]
 3) Akwai gidaje biyu da Allah ya shirya mana,
 Gidan Allah da gidan Shaiɗan.
 Idan baka gidan Allah, kana gidan Shaiɗan
 Samaniya ko jahanama.
 Korus

[V5]
 4) A wannan duniya ne za mu zaɓi gidanmu,
 Gidan Allah ko gidan Shaiɗan.
 Ayyukan da muke yi cikin wannan duniya.
 Su ne za su kaimu gidanmu.
 Korus

[V6]
 5) Idan ka bar gidan Allah kana gida na Shaiɗan.
 Dole ɗaya ya zama naka.
 Gidan Allah sai jin daɗi amma gida na Shaiɗan,
 Sai dai shan azaba sosai.
 Korus</lyrics>
</song>